Ayatullahi Khatami: Mahukuntan Saudiyya Suna Kokarin Kunna Wutan Rikici A Kasar Lebanon
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i25408-ayatullahi_khatami_mahukuntan_saudiyya_suna_kokarin_kunna_wutan_rikici_a_kasar_lebanon
Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Murabus da fira ministan Lebanon Sa'ad Hariri ya yi daga kan mukaminsa a kasar Saudiyya lamari ne da ke fayyace irin tsoma bakin da mahukuntan Saudiyya suke yi a harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.
(last modified 2018-08-22T07:00:58+00:00 )
Nov 10, 2017 15:30 UTC
  • Ayatullahi Khatami: Mahukuntan Saudiyya Suna Kokarin Kunna Wutan Rikici A Kasar Lebanon

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Murabus da fira ministan Lebanon Sa'ad Hariri ya yi daga kan mukaminsa a kasar Saudiyya lamari ne da ke fayyace irin tsoma bakin da mahukuntan Saudiyya suke yi a harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.

A hudubar sallar jum'arsa ta yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Ayatullahi Sayyid Ahmad Khatami ya fayyace cewa: Mahukuntan Saudiyya suna kokarin kunna wutan rikici da mummunar dambaruwar siyasa a kasar Lebanon, kamar yadda suke da hannu dumu-dumu a tashe-tashen hankulan da suke faruwa a kasashen Iraki, Siriya, Yamen da Lebanon.

Ayatullahi Khatami ya kara da cewa: A fili yake mahukuntan Saudiyya sun tilastawa Sa'ad Hariri yin murabus daga kan mukaminsa na fira ministan Lebanon ta hanyar karanta takardar da suka gabatar masa a matsayin jawabinsa lamarin da yake matsayin tsoma baki karara a harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.

Har ila yau Ayatullahi Khatami ya fayyace kame-kamen 'ya'yan gidan sarautar Saudiyya da mahukuntan kasar ke yi a matsayin wani sabon salon makirci. Kamar yadda furuci da barazanar da yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad bin Salman ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran zasu fuskanci maida martani mai gauni daga al'ummar Iran.