Larijani: Kasashen Iran, Turkiya Da Rasha Suna Kokarin Warware Rikicin Syria
Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr.Ali Larijani ya bayyana haka ne a jiya laraba a yayin ganawa da pira ministan kasar Turkiya Binali Yildirim.
Larijani wanda yake halartar taron kungiyar majalisun Asiya da ake yi a birnin Istanbul na kasar Turkiya, ya kuma ce; Aiki tare da kasashen uku suka yi ne ya kawo karshen ta'addanci wanda Amurka take goyawa baya.
Sai dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma yi ishara da yiyuwar bullowar wasu matsalolin a kasashen Yemen da kuma Lebanon, saboda amfani da karfi da wasu kasashe su ke yi.
Dr. Ali Larijani ya kuma yi tsokaci akan alakar tattalin arziki a tsakanin Iran da Turkiya tare da cewa a halin yanzu cinikayya a tsakaninsu ta tashi daga dalar Amurka biliyan 12 a shekara zuwa biliya 30.