Iran: Murkushe Da'ish, Gagarumar Nasara Ce A Kan Gwamnatin Amurka Da H.K.Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i25727-iran_murkushe_da'ish_gagarumar_nasara_ce_a_kan_gwamnatin_amurka_da_h.k.isra'ila
Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya bayyana cewa: Kawo karshen kungiyar ta'addanci ta Da'ish gagarumar nasara ce a kan makircin gwamnatin kasar Amurka da 'yar korenta haramtacciyar kasar Isra'ila.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 24, 2017 15:54 UTC
  • Iran: Murkushe Da'ish, Gagarumar Nasara Ce A Kan Gwamnatin Amurka Da H.K.Isra'ila

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya bayyana cewa: Kawo karshen kungiyar ta'addanci ta Da'ish gagarumar nasara ce a kan makircin gwamnatin kasar Amurka da 'yar korenta haramtacciyar kasar Isra'ila.

A hudubar sallar Juma'arsa ta yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Hujjatul-Islam Kazim Sadiqi ya bayyana cewa: Gwamnatin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila sun kafa kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce da nufin kunna wutan rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya amma sai mummunar aniyarsu ta kasa cimma nasara.

Hujjatul-Islam Sidiq ya kara da cewa: Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta tafka munanan ayyukan cin zarafin bil-Adama musamman aiwatar da dangogin kashe-kashen gilla mafi muni a tsawon tarihi da suka hada da fille kan mutane, kona su a raye, nutsar da mutane a cikin ruwa har su mutu, turo su daga kan dogayen benaye, tada bama-bamai a cikin Masallatai da wajajen taron jama'a da sauransu.

Har ila yau Hujjatul-Islam Kazim Sidiqi ya fayyace cewa: Makiya suna kokarin ganin sun bata sunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a idon duniya amma kullum kasar sai samun ci gaba take yi a bangarori da dama.