Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Ya Gana Da Shugaba Ruhani
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i26199-sakataren_harkokin_wajen_birtaniya_ya_gana_da_shugaba_ruhani
Sakataren harkokin wajen kasar Britania Boris Johnson ya gana da shugaba Hassan Ruhani a nan Tehrana a yau Lahadi
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Dec 10, 2017 07:38 UTC
  • Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Ya Gana Da Shugaba Ruhani

Sakataren harkokin wajen kasar Britania Boris Johnson ya gana da shugaba Hassan Ruhani a nan Tehrana a yau Lahadi

Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa da dama, daga ciki har da yadda kasashen biyu zasu aiwatar da yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran wacce ake kira (JCPOA) a takaice, da kuma matsalolin da yankin gabas ta tsakiya ta ke fama da su.

A jiya Asabar ne sakataren harkokin wajen kasar ta Britania ya iso birnin Tehran, inda a jiya din ya gana da takwaransa na kasar Iran Mohammad Jawad Zareef, da Ali Larijani kakakin majalisar dokokin kasar Iran da kuma Ali Akbar Salihi shugaban hukumar Nuklia ta kasar Iran. 

A tattaunawarsu da Johson wadan nan jami'an gwanatin Iran sun tabo batutuwan tattalin arziki, hulda tsakanin bankunan kasashen biyu da kuma harkokin tsaro a yankin.