Iran : Zarif Zai Ziyarci Turkiyya
Mar 19, 2016 07:21 UTC
Yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad- Javad Zarif ke fara wata ziyarar aiki ta yini guda a kasar Turkiyya.
Wannnan ziyara dai na nada nufin kara karfafa dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu da ma batutuwan da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.
A yayin ziyara tasa Mr Zarif zai gana da shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da kuma firiministan kasar Ahmet Davutoglu.
Wannan ziyara dai na daga cikin alkawuran da kasashen biyu sukayi kwanan baya yayin ziyara da firaministan Turkiyyar Ahmed Davutoglu ya kawo nan Teheran na kara karfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu.