Iran : Jagora Ya Taya Iraniyawa Murna Sabuwa Shekara
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i2686-iran_jagora_ya_taya_iraniyawa_murna_sabuwa_shekara
Yau ne al'ummar Iran ke bukukuwan shiga sabuwar shekara hijira shamsiyya ta 1395 da ake kira Nowroz.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 20, 2016 02:12 UTC
  • jagoran addini Iran
    jagoran addini Iran

Yau ne al'ummar Iran ke bukukuwan shiga sabuwar shekara hijira shamsiyya ta 1395 da ake kira Nowroz.

Ana dai gudanar da irin wannan bukuwan a duk fadin kasar da kuma kasashen da su ka yi tarayyar al’adu kamar su Afghanistan da Tajikistan da Kurdawa da kasashen yankin Asiya ta tsakiya.

A dalilin zagayowar sabuwar shekara, jagoran juyin juya halin kasar ta Iran Ayatollah Said Ali Khameinai ya isar da sakon murnarsa ga dukkan iraniyawa na ciki da wajen kasar, tare da yi masu fatan alhairi a duk inda suke.

Jagoran ya kara da cewa bai manta ba da duk iyalan shahidan kasar da wadanda suka samu raununa a yake-yaken da kasar tayi fama dasu dama duk wadanda sukayi gwagwarmaya wajen dora wannan kasar bisa turba ta gaskia irin su mirigayi Iman Khomaini.

A wannan sabuwa shekar data soma an dora ta bisa taken yar mazon Allah (SAW) Fatima (AS), wanda jagoran yayi fatan Allah yasa al'umma kasar suyi koyi da kyawawan halayen wannan baiwar Allah.