Sabuwar Siyasar Tsaron Kasar Amurka Da Zargi Maras Tushe Kan Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i27457-sabuwar_siyasar_tsaron_kasar_amurka_da_zargi_maras_tushe_kan_kasar_iran
A ranar Juma'ar da ta gabata ce sakataren tsaron kasar Amurka Jim Mattis ya gabatar da abin da suke kira "Dabarun Tsaron Kasar Amurka Na Shekara ta 2018", inda ya bayyana kasashen Rasha Da China a matsayin babbar barazana ga Amurka da kawayenta a fage na kasa da kasa, sannan a yankin Gabas ta tsakiya da Asiya kuma ya bayyana Iran da Koriya ta Arewa a matsayin manyan kalubalen da Amurkan take fuskanta a yankin.
(last modified 2018-08-22T07:01:18+00:00 )
Jan 21, 2018 03:15 UTC
  • Sabuwar Siyasar Tsaron Kasar Amurka Da Zargi Maras Tushe Kan Kasar Iran

A ranar Juma'ar da ta gabata ce sakataren tsaron kasar Amurka Jim Mattis ya gabatar da abin da suke kira "Dabarun Tsaron Kasar Amurka Na Shekara ta 2018", inda ya bayyana kasashen Rasha Da China a matsayin babbar barazana ga Amurka da kawayenta a fage na kasa da kasa, sannan a yankin Gabas ta tsakiya da Asiya kuma ya bayyana Iran da Koriya ta Arewa a matsayin manyan kalubalen da Amurkan take fuskanta a yankin.

A cikin wannan sabuwar dabarun tsaro na Amurkan mai shafukka 11, sau 6 aka ambaci sunan Iran, inda aka gabatar da wasu tuhumce-tuhumce marasa tushe kan kasar Iran din. Daga irin wadannan zarge-zargen har da bayyanar da Iran a matsayin tushen yada rikici da tashin hankali a yankin kana kuma babbar barazana ga tsaro da zaman lafiya yankin Gabas ta tsakiya. Hakan kuma an bayyana shirin nukiliyan Iran da kuma abin da suka kira goyon bayan ayyukan ta'addanci haka nan kuma da kokarin tabbatar da tasirinta a yankin ta mai da yankin ya zamanto waje mai cike da rikici da tashin hankali. Har ila yau kuma Amurkan ta bayyana cewar ma'aikatar tsaron kasar PENTAGON za ta ci gaba da kokari wajen dakile Iran da hana ta sakat ta hanyar hadin gwiwa da wasu kasashe na yankin.

Amurka tana gabatar da irin wadannan tuhumce-tuhumce marasa tushe ne a daidai lokacin da mafi yawa daga cikin masana da kuma al'ummomin yankin Gabas ta tsakiyan suna ganin Amurkan a matsayin ummul aba'isin duk wani tashin hankali da zubar da jinin da ke faruwa a yankin da nufin manufarta. Kamar yadda shi da da kansa shugaban Amurkan, musamman a lokacin da yake yakin neman zabe, ya zargi gwamnatin tsohon shugaban Amurkan Barrack Obama da kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta hanyar goyon baya da taimakon gwamnatin Saudiyya daya daga cikin manyan kawayen Amurka a yankin Gabas ta tsakiyan.

Dangane da tuhumar cewa Iran tana kokarin samar da wani yanayi da za ta fadada tasirinta  wanda hakan shi ne babban lamarin da ke haifar da rikici a yankin, idan har Amurkan tana magana ne kan kasashe da kungiyoyin gwagwarmaya wadanda suka zamanto babbar barazana ga haramtacciyar kasar Isra'ila, to wannan kan wani lamari ne da Iran take alfahari da kuma takama da shi. Haka nan dangane da shirin makamanta masu linzami na kariya kuwa, wannan shi ma wani batu ne da Iran din ba ta boye shi ba kuma ta  sanar da shi a matsayin daya daga cikin hanyoyin da take bi wajen kare kanta daga duk wani kokari na wuce gona da iri a kanta daga wajen makiyanta.

A takaice dai irin wadannan tuhumce-tuhumce da Amurkan take yi wa Iran ba wani sabon abu ba ne wani batu ne da shekaru aru-aru take yinsa sai dai kuma hakan bai hana Iran ci gaba da abin da ta sa a gaba ba na kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin Gabas ta tsakiyan wanda shi kansa hakan wani lamari ne da ke tabbatar mata da zaman lafiya da kwanciyar hankalinta.