Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Birnin Brussels
Mar 22, 2016 23:15 UTC
-
Sadiq Ansari Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai a birnin Brusees, tare da isar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Sadiq Hussain Jabiri Ansari ya bayyana cewa, harin da aka kai a birnin Brussels ya kara tababtar da cewa barazanar ta'addanci ta shafi kowane bangaren na duniya.
A kan haka ya ce ya zama a kan al'ummomin duniya da su hada karfi karfe domin tunkarar irin wannan ta'addanci da ke samo asali daga tsattsauran ra'ayi da jahilci, tare da tabbatar da cewa hanyar yin hakan ita ce taka birki ga masu kare ta'addanci a siyance da kuma ta fuskar akida, tare da ba su makudan kudade.