Zarif: Amurka Na Hana Turawa Aiki Da Wani Sashe Na Yarjejeniyar Nukiliya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i28783-zarif_amurka_na_hana_turawa_aiki_da_wani_sashe_na_yarjejeniyar_nukiliya
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya fadi cewa iran tana aiki da dukkanin abin da ya rataya a wuyanta na yarjejeniyar Nukiliya.
(last modified 2018-08-22T07:01:30+00:00 )
Mar 04, 2018 15:28 UTC
  • Zarif: Amurka Na Hana Turawa Aiki Da Wani Sashe Na Yarjejeniyar Nukiliya

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya fadi cewa iran tana aiki da dukkanin abin da ya rataya a wuyanta na yarjejeniyar Nukiliya.

Muhammad Jawad Zarif ya kuma bayyana cewa; Amurka ba ta aiki da yarjejeniyar Nukiliyar sannan kuma tana hana kasashen wuri aiki da wasu sassa na yarjejeniya.

Da yake magana akan ziyarar da ministan harkokin wajen Faransa zai kawo Iran, Muhammad Jawad Zarfi ya ce; Muna yin tattaunawa da dukkanin kasashen da muke da alaka da su ta fuskokin siyasa da tattalin arziki." Bugu da kari ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Daga cikin batutuwan da bangarorin biyu za su tattauna akansu da akwai abubuwan da suke faruwa a fagen siyasar gabas ta tsakiya.

A gobe litinin ne ake sa ran ministan harkokin wajen na kasar Faransa  Jean-Yves Le Drian zai kawo ziyara Iran.