Ganawar Rauhani Da Nawaz Sharif A Islam-abad
-
Ziyarar Shugaba Rauhani A Pakistan
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani wanda ya fara ziyarar aikia yau kasar Pakistan, ya gana da Firayi ministan kasar Nawaz Sharif a birnin Islam-abad.
Shugaba Rauhani ya isa kasar ta Pakistan ne a yau tare da wata babbar tawaga da ta kunshin ministoci da kuma manyan jami'a a bangarori daban-daban, inda Firayi minista Nawaz Shafi tare da tawagarsa suka tarbi Shugaba Rauhani a a yau a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Islam-abad.
Bayan kammala ganawa tsakanin Rauhani da Nawaz Sharif a yau, an sanya hannu kan yarjeniyoyi tsakanin kasashen Iran da Pakistan kan lamurra da suka shafi siyasa, kasuwanci, bunkasa harkokin tattalin arziki, tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da sauransu.
A gobe ne shugaba Rauhani zai gana da shugaban kasar ta Pakistan Mamnun Hussain, tare da wasu daga cikin manyan jami'an kasar, gami da malaman jami'oi da kuma malaman addini.