Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Mutuwar Winnie Mandela
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i29598-ministan_harkokin_wajen_iran_ya_aike_da_sakon_ta'aziyyar_mutuwar_winnie_mandela
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya aike wa gwamnati da kuma al'ummar kasar Afirka ta Kudu da sakon ta'aziyyar mutuwar matar tsohon shugaban kasar kuma jagoran fada da wariyar launin fata, Nelson Mandela, wato Uwargida Winnie Mandela.
(last modified 2018-08-22T07:01:39+00:00 )
Apr 03, 2018 12:50 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Mutuwar Winnie Mandela

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya aike wa gwamnati da kuma al'ummar kasar Afirka ta Kudu da sakon ta'aziyyar mutuwar matar tsohon shugaban kasar kuma jagoran fada da wariyar launin fata, Nelson Mandela, wato Uwargida Winnie Mandela.

A yau Talata ce ministan harkokin wajen na Iran ya aike da sakon ta'aziyyar inda a ciki ya bayyana cewa: Rashin uwargida Winnie Mandela babban rashi ne ba wai kawai ga kasar Afirka ta Kudu ba da nahiyar Afirka ba, face dai ga dukkanin al'ummomin duniya wadanda suke ganin tunani da akidar Nelson Mandela a matsayin wani abu mai karfafa musu gwiwa a fadar da suke yi na neman 'yanci da kuma nuna wariya.

Haka nan yayin da yake ishara da irin gwagwarmayar da Winnie Mandela ta yi musamman tsayin dakan da tayi wajen kasancewa tare da tsohon mijin nata, Nelson Mandela, Dakta Zarif ya ce yana isar da sakon ta'aziyya da alhininsa ga dukkanin iyalai, al'ummar Afirka ta Kudu da kuma dukkanin masoyanta saboda wannan rashi da aka yi.

A jiya Litinin ne dai aka sanar da mutuwar Uwar gida Winnie Mandela din tana da shekaru 81 a duniya sakamakon rashin lafiyar da ta jima tana fama da shi.