Janar Rashid: Kada Wata Kasa Ta Yi Gigin Jaraba Hakurin Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i29722-janar_rashid_kada_wata_kasa_ta_yi_gigin_jaraba_hakurin_iran
Babban kwamandan bataliyar dakarun IRGC ta Khatamul Anbiya a kasar Iran Janar Gholam Ali Rashid ya bayyana cewa; shirin da Iran take da shi na kariya, tana kwatankwacinsa na kai farmaki a kan duk wanda ya yi shishigi a kanta.
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 08, 2018 02:01 UTC
  • Janar Rashid: Kada Wata Kasa Ta Yi Gigin Jaraba Hakurin Iran

Babban kwamandan bataliyar dakarun IRGC ta Khatamul Anbiya a kasar Iran Janar Gholam Ali Rashid ya bayyana cewa; shirin da Iran take da shi na kariya, tana kwatankwacinsa na kai farmaki a kan duk wanda ya yi shishigi a kanta.

janar Rashid ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wani rangadi a wuraren tsaro na kasar Iran a kan iyakokinta na ruwa a yankin tekun fasha, inda ya gana da manyan kwamnadojin da ke kula da ayyukan tsaro na rundunar sojin Iran a yankin.

Ya ce ko shakka babu Iran tana fatan ganin an samu tsaro da zaman lafiya a dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, amma kuma a lokacin guda tana sanya ido da kyau a kan dukkanin abubuwan da suke wakana a yankin baki daya, kuma ba za ta taba yarda da duk wata barazana  a kan nata tsaron ba.

Janar rashidi ya ce sun shirya tsaf domin kare kasarsu daga duk wani shishigi, kamar yadda kuma a shirye suke suka farmaki a kan duk wanda ya taba su.

Ya kara da cewa yana yin kira ga masu tuannin yin shishigi a kan kasar Iran, da kada su yi gigin jaraba hakurin kasar ta Iran, domin yin hakan ba abu ne mai kyau ga yankin gabas ta tsakiya baki daya ba.