Shirin Kasashen Iran Da Senegal Na Bunkasa Harkar Tattalin Arziki A Tsakaninsu
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i29804-shirin_kasashen_iran_da_senegal_na_bunkasa_harkar_tattalin_arziki_a_tsakaninsu
A ziyarar aikin da ya shirya gudanarwa a kasashen nahiyar Afrika da na Latin Amurka: Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tawagar da ke rufa masa baya sun isa birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.
(last modified 2018-08-22T07:01:41+00:00 )
Apr 11, 2018 02:12 UTC
  • Shirin Kasashen Iran Da Senegal Na Bunkasa Harkar Tattalin Arziki A Tsakaninsu

A ziyarar aikin da ya shirya gudanarwa a kasashen nahiyar Afrika da na Latin Amurka: Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tawagar da ke rufa masa baya sun isa birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.

A ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Muhammad Jawad Zarif da mahukuntan kasar Senegal, bangarorin biyu sun tattauna batun bunkasa alakar tattalin arziki a tsakaninsu musamman batun harkar kasuwanci ta hanyar musayar kayayyaki a tsakanin kasashensu.

A yayin zaman tattaunawa tsakanin tawagar kasar Iran da na Senegal sun fi maida hankali ne musamman kan harkar kasuwanci da ta shafi man fetur, wutan lantarki, kayayyakin abinci, kera motoci, musayar kwarewa a fannin kimiyya da fasaha da sauransu. A fili yake cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran baya ga matakin karfafa alakar jakadancinta da kasashen duniya tana kuma kokarin ganin ta bunkasa alakarta da su a fagen tattalin arziki.

A jawabinsa ga zaman hadin gwiwa da ya gudana tsakanin tawagar kasar Iran da ta hada da jami'an jakadanci da na tattalin arziki da kuma tawagar kasar Senegal a ranar Litinin da ta gabata a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal: Dr Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Senegal a matsayinsu na kasashe biyu masu muhimmanci a yammacin Asiya da kuma yammacin nahiyar Afrika kuma mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C zasu iya hada karfi da karfe wajen taka gagarumar rawa a fagen bunkasa harkar tattalin arziki a yankunansu tare da karfafa matakan zaman lafiya da sulhu da kuma hadin kan al'ummar musulmin duniya.

Dr Jawad Zarif ya kara da cewa: Karfafa alaka a tsakanin kasashen Iran da Senegal musamman a harkar kasuwanci da musayar fasaha da kwarewa, wata babbar dama ce ta biyan bukatun junansu tare da karfafa gwiwar 'yan kasuwar kasashen biyu.

Sakamakon haka karfafa alakar jakadanci da na harkar tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afrika gami da na Latin Amurka wata babbar dama ce ta gudanar da taimakekkeniya a tsakanin dukkanin bangarorin. Kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran take shirye ta taka gagarumar rawa a fagage da dama a nahiyar Afrika da kuma Latin Amurka a bangarorin harkar noma, gina madatsun ruwa, karfafa masana'antu, harkar man fetur da gas, fannin lafiya da kuma kere-kere da sauransu.

Haka nan a ci gaba da gudanar da ziyarar aikinsa a kasashen Brazil, Uruguay da Namibia: Dr Jawad Zarif zai rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da mahukuntan kasashen kan harkar kasuwanci, ilimi da al'adu, saboda babbar manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce samun kyakkyawwar alaka tsakaninta da kasashen duniya da nufin habaka zaman lafiya da sulhu tare da bunkasa harkar tattalin arziki a bangarori da dama.