Shugaba Rauhani: Musulunci Addinin Zaman Lafiya Da Kyawawan Dabi'u Ne
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i2986-shugaba_rauhani_musulunci_addinin_zaman_lafiya_da_kyawawan_dabi'u_ne
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani, ya bayyana cewa addinin musulunci addinin zaman lafiya da kyawawan dabi'u da fahimtar juna ne.
(last modified 2018-08-22T06:58:02+00:00 )
Mar 26, 2016 23:05 UTC
  • Shugaba Rauhani: Musulunci Addinin Zaman Lafiya Da Kyawawan Dabi'u Ne

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani, ya bayyana cewa addinin musulunci addinin zaman lafiya da kyawawan dabi'u da fahimtar juna ne.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban daruruwan manyan malaman jami'a da masana a birnin Islam-abad na kasar Pakistan.

Ya ce ya zama wajibi malaman addinin muslunci da sauran masana musulmi su bayar da dukaknin gudunmawarsu wajen ganin musulmi sun fuskanci hakikanin abin da ke ci musu tuwo a kwarya a matsayinsu na al'umma guda a duniya, tare da taka birki ga duk wani bangare da ke kokarin rarraba kan wannan al'umma.

Kamar yadda ya yi ishara da cewa abubuwan da suke faruwa yanzu a wasu kasashen musulmi kamar Yemen, Syria Iraki da sauransu, ya sanya Isra'ila da saura makiya musulunci sun samu kwanciyar hankali, domin kuwa a halin yanzu musulmin ne da kansu suka shagaltu da kansu.