Halayen Amurka Da Kuma Mahangar Jagora A Kansu.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i30692-halayen_amurka_da_kuma_mahangar_jagora_a_kansu.
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminai, a jawabin da ya gabatar a jiya Laraba dangane da ranar Malaman makaranta a nan Tehran ya yi wasu bayanai masu muhimmanci dangane da Amurka da kuma shirin Nukliyar kasar Iran.
(last modified 2018-08-22T07:01:48+00:00 )
May 10, 2018 03:37 UTC
  • Halayen Amurka Da Kuma Mahangar Jagora A Kansu.

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminai, a jawabin da ya gabatar a jiya Laraba dangane da ranar Malaman makaranta a nan Tehran ya yi wasu bayanai masu muhimmanci dangane da Amurka da kuma shirin Nukliyar kasar Iran.

Jagoran ya bayyana cewa a jawabin da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi a ranar Talata inda ya bayyana ficewar gwamnatin Amurka daga yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran, ya yi karaya dangane kasar Iran har fiye da 10 kafin ya yi barazana ga kasa da kuma mutanen kasar Iran.

Aya. Sayyid Khamina'i ya kara da cewa adawar da gwamnatin kasar Amurka bata takaita ga jagora da kuma jami'an gwamnatin kasar Iran ba, sai dai ta haka har da mutanen kasar wadanda suka zabi tsarin musulunci suke kuma ci gaba da kare shi.

Babban abinda yake damun Amurka dangane da Jumhuriyar musulunci ta Iran shi ne tana son ganin bayan tsarin musulunci da iko da kasar kimanin shekaru 40 da suka gabata, sannan ta sake dawowa kan shugabancin kasar Iran don kwasar arzikin kasar kamar yadda ta yi a da. Kuma Amurka ta bi hanyoyi bila adadin don cimma wannan manufar tata, amma ta kasa.

Daga cikin hanyoyin da Amurka take son bi don cimma manufofinta dangane da kasar Iran akwai shirin kasar Iran na makamashin Nukliya ta zaman lafiya da kuma bata dangantakar kasar da kasashen Turai. Wannan halin dai ya tabbatar da cewa Gwamnatin Donal trump bata fahinci kasa da kuma mutanen kasar Iran ba, fahinta na gaskiya. 

Jargoran ya kara da cewa matakin da Trump ya dauka na ficewa daga yerjejeniyae shirin Nkliyar kasar Iran wauta ce, wacce bata bamu mamaki ba. 

Ya ce hatta a lokacin shugabancin Barak Obama, wanda yake rubuta mana wasiki yake kuma jawabai na yaudara da nuna cewa da gaske yake manufarsa ba tumbuke Jumhuriyar musulunci a Iran ba, abinda yake bayyana halayen gwamnatocin Amurka basu boyu ga mutanen kasar Iran. 

Duk da cewa ficewar Amurka daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, ficewar wani bangare ne daga kasashen da aka kulla yerjejeniyar da su, sai dai muna iya daukarshi a matsayin barzana ga iran da kuma yankin gaba daya. 

Jagoan ya ce " ni ban amince da wadannan kasashe guda, ukku ba don haka bana dogro da alkawuransu, saboda suna aiki sabanin tsarin aikin diblomasia. Kasashen Turai a zahiri suna cewa suna da yencin wajen gudanar da lamuransu kamar yadda suke so, sai dai fatammu shi ne kada su fa cikin tarkon kasar Amurka da kuma wasu kasashen Larabawa na yankin tekun farisa, a kokarinsu na cutar da kasar Iran.

Kamar dai yadda wani masanin harkokin gabas ta tsakiya Gharth Purter yake cewa, yanzu sai mu jira mu gan abinda kasashen turai zasu yi.