Mataimakin Babban Sakataren Hukumar IAEA A Bangaren Bincike Ya Ajiye Aikinsa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i30738-mataimakin_babban_sakataren_hukumar_iaea_a_bangaren_bincike_ya_ajiye_aikinsa
Hukumar IAEA mai sanya ido a kan ayyukan nukliya ta duniya ta bada sanarwan cewa mataimakin babban sakataren hukumar a bangaren tsaro da bincike ya ajiye aikinsa.
(last modified 2018-08-22T07:01:49+00:00 )
May 12, 2018 04:44 UTC
  • Mataimakin Babban Sakataren Hukumar IAEA A Bangaren Bincike Ya Ajiye Aikinsa

Hukumar IAEA mai sanya ido a kan ayyukan nukliya ta duniya ta bada sanarwan cewa mataimakin babban sakataren hukumar a bangaren tsaro da bincike ya ajiye aikinsa.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa babban sakataren hukumar Yukiya Amano ya maye gurbin Tero Varjoranta da Massimo Aporo wanda ya kasance mataimakinsa a bangaren bincike na hukumar a jiya Jumma'a.

Labarin ya kara da cewa  Tero Varjoranta yana shugabancin wannan bangaren na hukumar ta IAEA tun shekara ta 2013, sannan ya kara da cewa ajiye aikin nasa baya rasa nasaba da rashin amincewar Amurka da yadda yake gudanar da aikinsa na bincike a kan shirin nukliyar kasar Iran.

Wani jami'an hukumar ta IAEA wanda baya son a bayyana sunansa ya ce  Tero Varjoranta bai bayyana dalilan ajiye aikin nasa, amma ya tabbatar da cewa wanda ya maye gurbinsa zai ci gaba da aikin hukumar a wannan bangaren ba tare da wata matsala ba.