Jami'an Tsaron Kasar Iran Sun Yi Nasarar Murkushe Wasu Gungun 'Yan Ta'adda
(last modified Wed, 30 May 2018 19:34:14 GMT )
May 30, 2018 19:34 UTC
  • Jami'an Tsaron Kasar Iran Sun Yi Nasarar Murkushe Wasu Gungun 'Yan Ta'adda

Kwamandan rundunar tsaro a lardin Sistan Baluchestan da ke shiyar kudu maso gabashin kasar Iran ya sanar da murkushe wasu gungun 'yan ta'adda a garin Saravan da ke lardin.

Brigadier Janar Muhammad Ghanbari kwamandan jami'an tsaro a lardin Sistan Baluchestan a yau Laraba ya sanar da cewa: Jami'an tsaron Iran sun yi wani gumurzu da wasu gungun 'yan ta'adda a kan iyakar garin Saravan, inda suka yi nasarar fatattakan 'yan ta'addan tare da halaka daya daga cikinsu.

Muhammad Ghanbari ya kara da cewa: Bayan fatattakan 'yan ta'addan a gano tarin makamai a maboyansu da suka hada da manyan bindigogi da kanana gami da bama-bamai da kuma nau'o'in jigida na kai hare-haren kunan bakin wake.

Garin Saravan dai yana lardin Sistan Baluchestan na kasar Iran ce da ke kusa da kan iyaka da kasar Pakistan, sakamakon haka ake samun gungun 'yan ta'adda da suke tsallakowa zuwa cikin kasar Iran domin cimma mummunan burinsu na ta'addanci.