Jami'an Tsaron Iran Biyu Sun Yi Shahada
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i31462-jami'an_tsaron_iran_biyu_sun_yi_shahada
Jami'an tsaron kasar Iran biyu dake tsaron kan iyakar kasar sun yi shahada a yayin fafatawa da 'yan ta'adda a arewa maso yammacin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 06, 2018 02:47 UTC
  • Jami'an Tsaron Iran Biyu Sun Yi Shahada

Jami'an tsaron kasar Iran biyu dake tsaron kan iyakar kasar sun yi shahada a yayin fafatawa da 'yan ta'adda a arewa maso yammacin kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar ya habarta a daren jiya talata jami'an tsaron kasar Iran biyu dake tsaron kan iyakar kasar sun yi shahada a yayin fafatawa da 'yan ta'adda a arewa maso yammacin kasar.

Sanarwar ta ce lamarin ya auku ne a kan iyakar kasar dake jihar Azerbaijan ta yamma inda wasu gungun 'yan ta'adda suka yi kokarin shigowa cikin kasar.

A shekarar da ta gabata ma irin wannan al'amarin ya auku a yankin, inda 'yan ta'adda suka kashe wani adadi na jami'an tsaron kan iyakar kasar ta Iran.

Amurka da haramtacciyar kasar Iran gami da wasu kasashen larabawa a yankin na amfani da kuma taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda da masu fada da juyin juya halin musulinci ta kasar Iran, domin cimma manufinsu na yaki da tsarin musulinci a kasar Iran.