Siyasar Harshen Damo Na Kasashen Yamma A Mahangar Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana matsayar jamhoriyar musulinci ta Iran a tsakakin al'ummar Duniya, yayin da yake ganawar shan ruwa da wasu gungun malaman jami'a da sauran manyan makarantu na kasar a marecen lahadin da ta gabata.
A yayin da yake ishara kan matsayin jamhoriyar musulinci a idanun al'ummar Duniya, jagora ya bayyana cewa a tsakanin kasashe masu girman kai da marassa kima jamihriyar musulinci nada makiya masu yawan gaske, kamar yadda a tsakanin mafi yawan al'ummar yankin da mafi yawan kasashen Duniya, Iran nada matsayi mai girma, mutunci da kuma magoya baya masu yawa, da hakan ya sanya makiya ke ci gaba da yi mata makarkashiya, wanda kuma da falalar Ubangiji ba za su ci nasara a gaban al'ummar kasar Iran ba.
A wani bangare na jawabinsa jagora ya yi ishara kan siyasar harshen Damo na kasashen Yamma da kuma yadda suke taimakawa kasashen dake fice iyaka, da sakamakon hakan ya janyo Yaki da wanzuwar 'yan ta'adda, mamaya da rashin tsaro kan al'ummar yankin da ma Duniya gaba daya, kisan Mata da kananen yara a yankin Zirin Gaza, da kuma raba Palastinawa sama da miliyan biyar na daga cikin wannan wakiya maras dadi da ta wakana shekaru masu yawa kan al'ummar Palastinu.
A yayin da yake ishara kan nuna zalincin Shimir din na wannan zamani, Piraministan kisan kananen yara na mamaya wato Netanyahu a ziyararsa zuwa kasashen Turai ya bayyana cewa wannan dan ta'adda da yayi fice ga dukkanin azzalumai cikin tarihi ya tsulawa Shugabanin kasashen Turai, inda ya ce musu wai kasar Iran na son kawo karshen milyoyin yahudawa, alhali kuwa hanyar magance matsalar Palstinu ita ce hanyar da Duniya ta amice da ita a yau, wato bin hanyar Demokaradiya.
Jagora ya ce a halin yanzu dai tsarin dimokradiyya wani tsari da aka yarda da shi a duniya. Don haka ne muka ce al'ummar Palastinu da suka hada musulmi da kiristoci da yahudawansu wadanda su ne 'yan asalin kasar su ne ya kamata a bar musu ragamar ayyana makomarsu.
Jagoran ya ce kamata a yi a gudanar da kuri'ar jin ra'ayin al'ummar Palastinu wadanda suke wajen tun kimanin shekaru 100 da suka gabata kai ko ma da shekaru 80 ne, duk abin da suka zaba sai a aiwatar da shi. Jagoran ya ci gaba da cewa wannan ita ce kawai hanya ta adalci ta magance matsalar Palastinu.
Wannan kuma ita ce shawarar da jamhoriyar musulinci ta gabatar ga MDD, shin wannan shawara ta sabawa tsarin Duniya ne? to me ya sanya kasashen yamma suka ki fahimtar hakan? amsar wannan tambaya da tambayoyi da dama na daban na komawa ne kan siyasar harshen damo na kasashen yamma da suke ikrarin kare hakin bil-adama da kuma tafarkin Demokaradiya, alhali kuwa mafi yawa na ta'addancin da aka aiwatan kan Dan Adam a duniya daga wajen wadannan kasashe ne ko kuma kungiyoyin da suke goyawa baya.