Limamin Juma'a:Ya Bukaci Gwamnati Tayi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Fasadi.
Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na birnin Tehran ya bukaci gwamnati da ta dauki kwararen mataki na fada da masu fasadi.
Ayatollahi Ahmad Khatami Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na birnin Tehran ya yi ishara kan ganawar baya-bayan da jagoran musulinci yayi da tawagar gwamnati da kuma nasihohin da ya yi musu musaman kan kare manufofin juyin juya halin musulinci da kuma kiyaye shi ta hanyar dogaro da ababen da ake kerawa cikin gida da kuma zartar da tsarin nan na kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, ya ce wajibi ne a yi fada da duk wani nau'i na fasadi, musaman ma kan mutanan da suke fice iyaka da kudin baitul- mali na kasar.
Ayatollahi Ahmad Khatami ya ce dole ne a hukunta mai tsanani ga duk wani mutum da aka samu da laifin bata kudin gwamnati duk matsayinsa da mikaminsa da kuma duk wata cibiya da aka samu da lafin fasadi daidai yadda dokokin jamhoriyar musulinci suka tanada.
Yayin da yake ishara kan kwamitocin da aka kafa na yaki da fasadi, Ayatollahi Ahmad Khatami ya bukaci kwamitin ya yi aiki tsakani da Allah kuma ya mekawa magabatan kasar rahoto na gaskiya, sannan a bayyana al'umma masu kokarin yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa.