Limamin Tehran:Sadaukar Da Kan Yan Baya Ne Sirrin Zaman Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i32804-limamin_tehran_sadaukar_da_kan_yan_baya_ne_sirrin_zaman_lafiya
Wanda ya jagoranci Sallar juma'a anan Tehran ya bayyana cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake da shi a Iran a yanzu tushensa tsayin dakar fursunonin yaki
(last modified 2018-08-22T07:02:15+00:00 )
Aug 17, 2018 14:37 UTC
  • Limamin Tehran:Sadaukar Da Kan Yan Baya Ne Sirrin Zaman Lafiya

Wanda ya jagoranci Sallar juma'a anan Tehran ya bayyana cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake da shi a Iran a yanzu tushensa tsayin dakar fursunonin yaki

Hujjatul-Islam Wal Muslimin Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi Far ya ce;A wannan lokacin tsayin dakar 'yan gwagwarmaya da fursunonin yaki sune tushen zaman lafiya a cikin kasashen Iran da Iraki da Syria.

Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma ta hanyar dogaro da sadaukar da kan da maganatan su ka yi Iran tana iya warware matsalolin da take fuskanta a wannan lokacin

Limamin na Tehran ya kuma tabo halin da kasar Yemen take ciki sannan ya ce; Al'ummar duniya sun yi shiru akan bala'in da mutanen kasar su ka fada balle su ba su kariya.