Sep 10, 2018 07:27 UTC

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al'amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau.

A cikin makon dai an gudanar da wasu muhimman tarurruka guda biyu a nan birnin Tehran. Na farko dai shi ne taron da 'yan majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran suka gudanar don tattauna batutuwa daban-daban da kuma ganawar da  suka yi da Jagoran juyin juya halin Musulunci. Na biyu kuma shi ne taron shugabannin kasashen Iran, Rasha da Turkiyya da aka  gudanar a nan Tehran, wadanda suna daga cikin lamurran da suka dau hankula a kasar Iran cikin makon. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali don jin yadda shirin na mu na yau zai kasance inda za mu fara da batun jagoran 'yan majalisar kwararrun.

--------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Majalisar kwarrru ta jagoranci dai wata cibiya ce mai muhimmancin gaske a tsarin siyasa na  kasar Iran wacce tun a farko-farkon kafa jamhuriyar Musulunci a kasar ta Iran bayan tsara kundin tsarin mulkin kasar aka gabatar da magana kanta da muhimmancin kafa ta.

Daga cikin ayyuka da nauyin da ke wuyan membobin wannan majalisar dai a matsayinsu na zababbun al'umma, baya ga nauyi mai matukar girma da muhimmanci da ke wuyansu na zaban Jagoran juyin juya halin Musulunci a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, har ila yau kuma suna da wani nauyin na sanya ido kan yadda lamurra suke gudana a cikin kasa. Hakan ne ya sanya majalisar ta kasance daga cikin cibiyoyi masu matukar muhimmancin gaske a tsarin Jamhuriyar Musulunci da ke gudana a kasar ta Iran.

A saboda haka ne bayan gama wannan taron da suke yi, to kamar yadda aka saba su kan gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci don gabatar masa da rahoto kan zaman na su da kuma sauraren jawabin da zai yi.

A ganawar da yayi da 'yan majalisar kwararru a safiyar ranar Alhamis din da ta gabata, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin ishara da irin yanayi mai matukar muhimmanci da kuma hatsari da Iran take ciki a halin yanzu inda ya ce: "Tun bayan kafa tsarin Musulunci da kuma riko da wani sabon tafarki da kuma gabatar da wata sabuwar mahanga ta daban, tsawon shekaru arba'in din da suka gabata, ya ci gaba da gudanar da ayyukansa sabanin abin da ma'abota girman kan duniya suke so. A irin wannan yanayin sannan kuma a fagen siyasa ta kasa da kasa da ke cike da rikice-rikice da ake ciki,  hakan ya sanya wajibi ne a yi taka-tsantsan da kuma gudanar da ayyuka daidai da yadda yanayin yake".

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A halin yanzu dai gwamnatin Musulunci tana fuskantar wani yaki ne mai girma na tattalin arziki wanda ake jagorantar hakan daga wata cibiya ta waje sannan kuma da dukkan karfi ake yin hakan. Baya ga hakan, a bangare guda kuma akwai wani yakin na kafafen watsa labarai da farfaganda da ake yi wanda a mafi yawan lokuta a kan gafala daga ba shi muhimmanci.

Amurka ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban tana ta kokari wajen cutar da Iran. Wannan makircin na Amurka kuwa ya samo asali ne tun daga lokacin kallafaffen yakin Iran da Iraki wanda ta dauke shi a matsayin wata hanya ta cutar da Iran da kuma cimma bakar aniyarta a kan kasar, sannan kuma har ya zuwa yanzu din nan tana ci gaba da hakan. A halin yanzu dai Amurkan tana fakewa ne da batun makamai masu linzami na Iran din bayan da a baya ta fake da batun shirin makamashin nukiliya da kasar da kuma batun take hakkokin bil'adama.

A saboda haka ne wanann shi ne abin da taron makon da ya wuce na 'yan majalisar kwararru ya fi ba shi muhimmanci, don kuwa tushen abin da aka tattauna din shi ne batun tattalin arziki da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsalar.

----------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Har ila yau a ranar Juma'ar da ta gabata ce birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran din, ya dau bakuncin taron shugabannin kasashen Iran, Rasha da Turkiyya.

Daya daga cikin manufofin wannan taro dai da ta gudana tsakanin shugaban kasar Iran, Dakta Hasan Rouhani, Vladimir Putin na kasar Rasha da kuma Rajab Tayyib Erdogan na kasar Turkiyya ita ce tattaunawa kan hanyoyin magance rikicin kasar Siriya da kuma hanyoyin da za a bi wajen dakatar da ayyukan ta'addancin da ke gudana a kasar.

Jim kadan bayan gama taron shugabannin uku sun fitar da wata sanarwar bayan taro wacce ta kumshin azamar da suke da ita na aiki tare wajen kawo karshen kungiyoyin ta'addancin nan na Daesh, Jabhatun Nusra da sauran kungiyoyin ta'addanci da suke cikin kasar Siriyan.

Har ila yau kasashen uku suna ganin hanya guda ta magance matsalar kasar Siriya ita ce tattaunawa da cimma matsaya tsakanin dukkanin bangarori na siyasa na kasar. A don haka ne bangarori uku suka yi kira da ci gaba da gudanar da tarurruka na tattaunawa tsakanin al'ummar kasar Siriya kamar yadda ya zo cikin kuduri mai lamba na 2254 na kwamitin tsaron MDD.

Har ila yau kuma taron na Tehran ya jaddada rashin amincewa da yadda Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila suke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Siriya wanda suka ce wajibi ne a kawo karshen hakan.

Kasar Iran dai kamar yadda shugaba Rouhani ya bayyana ta yi amanna da cewa hanya guda kawai ta magance rikicin kasar Siriya shi ne abar al'ummar kasar su zaba wa kansu makomarsu ba tare da tsoma bakin wata kasa. Kamar yadda kuma shugaba Rouhanin ya ce Iran ta shiga kasar Siriya ne bisa bukatar da gwamnatin kasar ta gabatar mata da nufin fada da kungiyoyin ta'addancin da aka jibge su a kasar wadanda kuma suke ci gaba da zama barazana ga kasar da kuma sauran kasashen yankin.

------------------/

Har ila yau kuma a ranar Juma'ar da ta gabata din ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan da 'yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma. A yayin ganawar Jagoran ya bayyana cewar: Ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suna tsananin adawa da duk wani hadin kai da aiki tare tsakanin kasashen musulunci da kuma tabbatar da wani karfi na Musulunci.

Jagoran ya bayyana cewa irin wannan damuwar ita ce asalin dalilin kiyayyar da Amurka take yi da kasashen musulmi don haka sai ya ce: Iran da Turkiyya wasu kasashe ne masu mutumci da kuma karfi a yankin nan sannan kuma suna da fata mai kyau ga duniyar musulmi. A saboda haka wajibi ne su karfafa alakar da ke tsakaninsu a fagen siyasa da tattalin arziki.

Har ila yau a yammacin ranar Juma'a din dai jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da 'yan tawagarsa inda Jagoran ya bayyana fatan cewa taron da shugabanni ukun suka yi zai haifar da da mai ido. Jagoran ya bayyana cewar hadin kai da aiki tare da ake samu tsakanin Iran da Rasha a kan kasar Siriya wani lamari ne abin misali kana kuma wata alama da ke nuni da alaka mai kyau tsakanin kasashe.