Harba Makamai Masu Linzami Da Iran Ta Yi Wa Sansanonin 'Yan Ta'adda.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i33439-harba_makamai_masu_linzami_da_iran_ta_yi_wa_sansanonin_'yan_ta'adda.
Harba Makamai Masu Linzami Da Iran Ta YI Wa Sansanonin 'Yan Ta'adda.
(last modified 2018-10-02T04:04:36+00:00 )
Oct 02, 2018 04:04 UTC
  • Harba Makamai Masu Linzami Da Iran Ta Yi Wa Sansanonin 'Yan Ta'adda.

Harba Makamai Masu Linzami Da Iran Ta YI Wa Sansanonin 'Yan Ta'adda.

Da safiyar ranar Litinin ne dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka kai hari da makamai masu linzami akan sansanin 'yan ta'adda a kasar Syria a matsayin mayar da martani akan harin Ahwaz Harin an kai shi ne daga garin Kermansha da ke Iran zuwa yankin Bu-kamal da ke gabacin tafkin Furat.

A ranar 22 ga watan Disamba ne dai 'yan ta'addar Ahwaz da suke da goyon bayan kungiyar Da'esh da kuma kasashen Birtaniya da Saudiyya, sun kai hari akan sojoji da suke atisyae a garini Ahwaz wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 25 da jikkata wasu da dama.

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da 'yan wasan Iran da su ka wakilci kasar a wasannin Asiya, su ka dawo da kyautuka, ya ambaci harin na Ahawaz sannan ya kara da cewa:

'Wannan aiki ne na wadannan mutanen da aduk lokacin da su ka ci kasa a Syria da Iraki, sai Amurka ta cece su, kuma hannuwansu suna cikin aljihun kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa."

Jagoran juyin musuluncin ya ci gaba da cewa; "Tabbas, wadanda su ka kai harin Ahawz za su fuskanci sakamako mai tsanani."

Harin ta'addancin da aka kai wa Ahwaz ya zo ne bayan shan kashin da kungiyoyin 'yan ta'adda masu kafirta musulmi su ka yi a kasashen Irakida Syria; Don haka ya bayyana a fili cewa iyayen gidan 'yan ta'addar suna son ingizo su ne akan Iran.

A baya, ya bayyana a fili cewa Amurka ta kasance mai taimaka wa Kungiyoyin Taliban, Alqa'eda da Saddam da sauran masu wuce gona da Iri. A halin yanzu wannan kasar tare da kawayenta a wannan yankin, suna taimkawa 'yan ta'addar domin su haddasa rashin tsaro a cikin Iran.

Rawar da kasar Saudiyya ta taka a cikin lamari a fili yake, haka nan haramtacciyar kasar Isra'ila.

A baya ba da jimawa ba, Jaridar Independent ta Birtaniya ta buga rahoton da ya kunshi cewa:  Da akwai alaka bayyananniya a tsakanin kungiyoyi masu amfani da karfi, da Saudiyya ta fuskar kudade.

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya fadawa tashar talabijin din CNN cewa Saudiyya ta taka rawa a cikin samar da rashin tsaro a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya.

Wani abu da ya zama wajibi ga masu ruru wannan wutar su sani, shi ne cewa Iran za ta mayar da martani a gare su ta yadda za su yi nadama. Shekara daya da ta gabata, dakarun kare juyin musulunci sun mayar da martani akan harin da 'yan ta'adda su ka kawo a Tehran ta hanyar harba martani da makamai masu linzami akan sansanin 'yan ta'adda a yankin Deir alzur da ke Syria.

Harin da Iran din ta kai a safiyar jiya yana a matsayin martani ne akan harin na 'yan ta'adda a garin Ahawaz.