Iran A Shirye Take Ta Fuskanci Sabbin Takunkuman Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i33888-iran_a_shirye_take_ta_fuskanci_sabbin_takunkuman_amurka
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fuskanci sabbin takunkuman da Amurka take shirin dora mata a ranar Lahadi mai zuwa wato 4 ga watan Nuwamba.
(last modified 2018-11-02T09:50:47+00:00 )
Nov 02, 2018 09:50 UTC
  • Iran A Shirye Take Ta Fuskanci Sabbin Takunkuman Amurka

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fuskanci sabbin takunkuman da Amurka take shirin dora mata a ranar Lahadi mai zuwa wato 4 ga watan Nuwamba.

Majiyar muryar JMI ta nakalto kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Bahram Qasemi ya na fadar haka a safiyar yau Jumma'a ya kuma kara da cewa Manufar Amurka da takunkuman da take dorawa kasar Iran ita ce hana kasashen duniya da manya manyan cibiyoyin kudade da bankuna hulda da kasar. 

Qasemi ya kara da cewa Amurka ta kasa cimma wannan gurin nata ya zuwa yanzu a wasu wurare, ya kara da cewa a halin yanzu ma, sabbin takunkuman da Amurka zata dorawa kasar Iran a ranar 4 ga watan Nuwamba da muke ciki, ba za su kai Amurka ga manufar ta na hana kasar Iran saida danyen man fetur nata kwata-kwata a kasuwannin duniya ba.

Daga karshe kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ce tun kafin takunkumin na ranar 4 ga watan Nuwamba ya fara aiki ma ya gamu da cikas, don akwai kasashen da suka bayyana cewa ba zasu bi umurnin Amurka na daina sayan danyen man fetur na kasar Iran ba.