Limamin Tehran: Mamayar Ofishin Jakadancin Amurka A Tehran Sako Ne Gare Ta
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i34008-limamin_tehran_mamayar_ofishin_jakadancin_amurka_a_tehran_sako_ne_gare_ta
Wanda ya jagorancin sallar juma'a anan Tehran Hujjatul Islam Wal Muslimin Kazim Siddiqi ya yi ishara da ranar 13 ga watan Aban na hijira shamshiyya wanda ya bayyana a matsayin ranar da aka kaskantar da Amurka
(last modified 2018-11-09T15:35:19+00:00 )
Nov 09, 2018 15:35 UTC
  • Limamin Tehran: Mamayar Ofishin Jakadancin Amurka A Tehran Sako Ne Gare Ta

Wanda ya jagorancin sallar juma'a anan Tehran Hujjatul Islam Wal Muslimin Kazim Siddiqi ya yi ishara da ranar 13 ga watan Aban na hijira shamshiyya wanda ya bayyana a matsayin ranar da aka kaskantar da Amurka

Hujjatul-Islam Siddiqi ya kara da cewa; Mamaye ofishin jakadanci wanda cibiyar leken asiri ne da kuma kame jami'an diplomasiyyar Amurka sako ne mai girma da matasanmu su ka aike wa Amurka.

Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; Abin da ya faru a ranar 13 ga watan Aban wani batu ne mai matukar muhimmanci a siyasance kuma zai ci gaba da zama a haka a wurin al'ummar Iran.

Da ya tabo maganar takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran, limamin ya ce; SHekaru 40 kenan da suke kakaba mana takunkumi, amma duk da haka a karkashin takunkumin ne mu ka kera makamai masu linzami da makamai na tsaron kai sannan kuma muka mallaki manyan kamfanoni.

Limamin na Tehran ya kuma ce a yanzu an wayi gari Iran tana kera jiragen yaki da su jirage masu saukar angulu, domin mun daura damarar ganin mun zama masu cin gashin kansu.