Jagora: Hadin Kai Tsakanin Al'ummar Musulmi Wajibi Ne
(last modified Mon, 26 Nov 2018 05:34:18 GMT )
Nov 26, 2018 05:34 UTC
  • Jagora: Hadin Kai Tsakanin Al'ummar Musulmi Wajibi Ne

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa; hadin kai tsakanin al'ummar musulmi na duniya wajibi ne da ya rataya a kansu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da baki da suka halarci taron makon hadin kan musulmi da aka gudanar a birnin Tehran na kasar Iran, wanda kuma a jiya ne aka kammala taron karo na 32, wanda ake gudanarwa a kowace shekara a makon maulidin manzon Allah (SAW).

Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ci gaba da cewa, a kowane lokaci rayuwar manzon Allah (SAW) tana cike ne da darussa, wadanda yin aiki da abin da wadannan darussa suke koyarwa, ita ce mafita kuma hanyar warware dukkanin matsaloli da suke addabar al'ummar musulmi, a lokaci guda kuma idan musulmi suka ajiye wannan koyarwa ta manzon Allah mai cike da haske na shiriya, wadda take damfare da kur'ani mai tsarki, to kuwa musulmi za su yi ta cin karo da matsaloli a cikin lamurransu.

Ya ce akan haka, dole ne musulmi su koma zuwa ga yin riko da kur'ani mai tsarki, da kuma koyarwar manzon Allah a cikin dukkanin lamurransu a matsayin hanya daya tilo ta warware matsalolinsu, kuma hakan ba zai taba samuwa ba, har sai musulmi sun ajiye sabanin fahimta a gefe guda, sun hada kansu a kan addini guda daya shi ne musulunci,a  lokacin za su zama masu yin magana da kalma daya, kuma hakan shi ne babban makaminsu na rusa makircin makiya.

Daga karshe jagoran ya yi fatan alhairi ga dukkanin bakin da suka halarci wannan taro na makon hadin kai, da kuma taya su murna tare da sauran dukkanin sauran al'ummar musulmi na duniya, kan zagayowar wannan lokaci na murnar Maulidin manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi da alayensa tsarkaka.