An Gudanar Da Jana'izar Ayatullah Hashemi Shahrudi A Yau
An gudanar da jana'izar babban malamin addinin musulunci Ayatullah Mahmood Hashemi Shahrudi a yau, wanda Allah ya yi masa rasuwa a jiya a birnin Tehran.
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ya jagoranci sallar jana'izar wadda aka gudanar a birnin Tehran tare da halartar dubban daruruwan jama'a.
An bizne gawarsa a cikin hubbaren Sayyida Fatima Ma'asuma jikar Manzon Allah (SAW) da ke birnin Qom, inda kuma ake bizne gawawwakin manyan malamai da suka gabata a birnin tun daruruwan shekaru da suka gabata.
Mafi yawa daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Iran da manyan malamai sun halarci janazar, kamar yadda kuma akwai baki daga kasashen duniya daban-daban da suka halarci janazara a yau.
A daren yau kuma ana zaman karbar gaisuwar ta'aziyarsa a birnin na Qom, tare da manyan malamai da sauran jami'ai da al'ummar gari.