An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Richter 5.9 A Kudancin Iran
(last modified Sun, 06 Jan 2019 16:59:16 GMT )
Jan 06, 2019 16:59 UTC
  • An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Richter 5.9 A Kudancin Iran

Girgizan kasa mai karfin ma'aunun Richter 5.9 ta awkawa lardin kirmansha da ke iyaka da kasar Iraqi a kudancin kasar Iran a yau Lahadi.

Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa girgazar kasar wacce ta auku a yammacin yau Lahadi yana da zurgin kilomita 10 karkashin kisa daga garin Gilo a cikin lardin Kirmansha, sannan an ji karar aukuwarsa a biranen bagdaza, Najaf, Karbala, Diyala, Wasid, da arewacin kasar Iraqi da lardin Sulaimaniyya duk a cikin kasar Iraqi. 

Tuni dai ma'aikatan bada agajin gaggawa sun isa wurin da ta auku, amma har yanzun babu labarin irin asarorin da aka yi na rai ko na dukiya sanadiyar girgizan kasar. 

Girgizan kasa ta sha aukawa lardin kirmansha a cikin shekara guda da ta gabata, amma mafi munin su ita ce ta ranar 12 ga watan Nuwamban na shekara ta 2017 wanda ya lashe rayukan mutane 620 sannan wasu dubu 12 suka ji rauni