Shugaban Kasar Venezuela Ya Gana Da Ministan Tsaron kasar Iran
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya gana da ministan tsaron kasar Iran Manja janar Amir Hatamia jiya a birnin Caracas.
A yayin ganawar, Janar Hatami ya shedawa Maduro cewa, kasar Iran a shirye take ta yi aiki tare da kasar Venezuela domin kara bunkasa ayyukan tsaro.
Hatami ya ci gaba da cewa, kasashen Venezuela da Iran dukkaninsu suna fuskantar barazana iri daya ce daga kasashe masu girman kai, sakamakon siyasar da suka zaba ta su zama kasashe masu 'yanci, ba 'yan amshin shata na manyan kasashen duniya ba, domin kuwa matsin lambar da Venezuela ke fuskanta a yanzu, Iran ta kwashe shekaru 40 tana fuskantar irin wannan matsin lambar da takunkumai, amma hakan bai kara mata komai ba illa ci gaba.
A nasa bangaren shugaban kasar ta Venezuela Nicolar Maduro ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin kasashen Iran da Venezuela danganta ce da ta shafi dukaknin bangarori na ci gaban kasashen biyu.
A ranar Juma'a da ta gabata ce shugaba Maduro ya yi rantsuwar kama aiki a sabon wa;adin mulki na biyu, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a kasar a cikin watan Mayun 2018 da kashi 68 na kuri'un da aka kada, amma Amurka da wasu kasashe masu adawa da salon siyasar kasar ta Venezuela ba su amince da da hakan ba.