FBI Na Tsare Da Ma'aikaciyyar Tashar PRESSTV, Ta Iran, Marzieh Hashemi
(last modified Wed, 16 Jan 2019 07:23:32 GMT )
Jan 16, 2019 07:23 UTC
  • FBI Na Tsare Da Ma'aikaciyyar Tashar PRESSTV, Ta Iran, Marzieh Hashemi

An tsare Marzieh Hashemi, ‘yar jarida kuma ma’aikaciyar tashar talibijin din Press TV ta kasar Iran, a kasar Amirka ba tare da bayyana laifin da ta yi ba.

Tashar talibijin Press TV ya samu labarin cewar ana tsare da Marzieh Hashemi ne a wani wurin da ake tsare mutane a birnin Washington, duk da cewa har zuwa yanzu ba a caje ta da wani laifi ba.

 

‘Yar jaridar wacce ‘yar asalin kasar Amurka ce, ta tafi Amurkan ne don ziyartar dan’uwanta wanda ba yake fama da rashin lafiya da kuma sauran danginta, inda jami’an tsaron suka kama ta a filin jirgin sama na kasa da kasa na St. Louis Lambert a ranar Lahadi, daga kuma aka mika ta ga jami’an hukumar FBI, wadanda suka tsare ta.

 

Sama da sa’o’i 48 kenan, danginta ba su da labarinta, sai daga baya-bayan nan ne suka samu labarin cewa ana tsare da ita.

 

Duk da cewa babu wani cajin da aka gabatar mata, Marzieh Hashemin  ta shaidawa ‘yan’uwanta irin wulakanci da ake yi mata a inda ake tsare da itan. Inda ta ce an tilasta mata cire hijabinta  kuma ana mu’amala da ita kamar wata mai laifi.

 

Jami’an gidan yarin sun hana ta samun abicin Halal, a inda aka tilasta mata  rayuwa da burodi da biskit, na tsawon kwanaki.