Jahangiri:Duk Da Makircin Amurka, Iran Na Sayar Da Man Fetir
(last modified Mon, 21 Jan 2019 19:22:02 GMT )
Jan 21, 2019 19:22 UTC
  • Jahangiri:Duk Da Makircin Amurka, Iran Na Sayar Da Man Fetir

Mataimakin Shugaban Jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce: Duk da makircin da kasar Amurka ke kulawa na hana sayan man fetir din kasar da kuma hana shigo da kudi cikin kasar, Tehran na sayar da Man fetir din da take bukata.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Ishak Jahangiri mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran yayin da yake ziyara a lardin Kerman dake kudancin kasar a wannan Litinin na ishara da takunkumin zalincin da kasar Amurka ta kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce duk irin makarkashiyar da kasar Amurka ke kulawa kasar, mahukunta na amfani da wasu hanoyoyi na shigo na kudin Man fetir din da kasar ta sayar, da Magani da kayayyakin da  al'ummar kasar ke bukata.

Jahangiri ya kara da cewa, hukumomin Amurka na kokarin ganin sun katange jamhoriyar musulinci ta Iran da kuma matsin lamba kan al'ummar kasar, amma ba za su ci nasara ba.

Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya ce fitar da Amurka ta yi daga yarjejjeniyar nukiliyar da kasar Iran ta cimma da manyar kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus ya kara bakanta sunan Amurka a Duniya, yayin da kasar ta Iran ke samun daukaka a idanun al'ummar Duniya.

A yayin da yake ishara kan ci gaban da kasar Iran ta samu bayan shekaru 40 da juyin halin musulinci, Ishak Jahangiri ya ce a halin yanzu kasar ta kai inda ba ta dogara da ko wata kasar ba a fannoni daban-daban kama daga gine-ginen hanyoyin motoci, jirgin kasar, masana'antu, fasahar tecnologiya gami da na nukiliya.

har ila yau ya ce duk da firicin da Amurka ta yi na cewa Al'ummar kasar ba za su yi sallar cika shekaru 40 na juyin musulinci ba, shakka babu a shekarar bana Al'umma za su fito domin raya wannan salla fiye da shekarun da suka gabata.