Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Kai Ziyara Kasar Siriya
(last modified Mon, 28 Jan 2019 19:22:46 GMT )
Jan 28, 2019 19:22 UTC
  • Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Kai Ziyara Kasar Siriya

Mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya kai ziyara kasar Siriya, inda ya samu kyakkyawar tarbe daga Piraministan kasar a birnin Damuscus.

A marecen wannan Litinin ne mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Ishak Jahangiri ya fara wata ziyarar aiki a birnin Damuscus, inda ya samu kyakkyawan tarbe daga Piraministan kasar Imad Khamis, bayan rera taken jamhoriyar musulinci ta Iran da na kasar Siriya, Jahangiri da Khamis da tawagar dake bayansu sun isa wurin da aka tsara musu liyafa ta musaman.

Bayan kamala liyafar, mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Ishak jahangiri da Piraministan kasar ta Siriya Imad Khamis sun tattauna  a game da canjin da aka samu a yanki, da kuma siyasar Duniya a yankin.

Ana sa ran tawagar da mataimakin shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ta yi kwanaki biyu a birnin Damuscus, bayan ganawa da shugaban kasar ta Siriya Bashar Asad, Ishak jahangiri tare da tawagarta sa za su halarci taron hadin gwiwa na tattalin arziki tsakanin Iran da Siriya karo na 14.

Har ila yau ana sa ran bangarorin biyu za su sanya hanu kan ci gaba da yarjejjeniyar aiki tare a bangaren tattalin arziki, bayan kamala taron.