Iran A Shirye Take Ta Koma Aikin Gasa Makamashin Uranium A Kasar.
(last modified Sun, 10 Feb 2019 19:10:44 GMT )
Feb 10, 2019 19:10 UTC
  • Iran A Shirye Take Ta Koma Aikin Gasa Makamashin Uranium A Kasar.

Hukuma Mai Kula da makamashin nukliya a kasar Iran ta bayyana cewa a shirye take ta gasa karin makamashin uranium har zuwa soo 190,000.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban hukumar ta makamashin nukliya na kasar, mai kula da bangaren kasa da kasa yana cewa ganin yadda kasashen turai suke sabawa alkawarin da kasar Iran ta cimma da su kan yerjejenitar shrin nukliyar kasar, hukumarsa a shirye take ta fara gasa makamashin uranuim har zuwa soo 190,000 idan bukatar haka ta kama. 

Behruz Kamalvandi ya bayyana haka ne a yau Lahadi a lokacinda yake bude wata cibiya ta gwaje-gwajen ilmin kimiya a birnin Qazwin dake yammacin birnin Tehran. 

Kamalwandi ya ce a halin yanzu hukumarsa ta sami wasu sabbin kayakin aiki don gasa makamashin uranium da sauri kuma mai inganci. Don haka a duk lokacinda gwamnatin kasar ta tsaida shawara kan yin haka hukumar zata fara aikinta ba tare da bata lokaci ba.