Zarif Ya Gana Da Sayyid Hassan Nasrullah
(last modified Thu, 14 Feb 2019 08:11:47 GMT )
Feb 14, 2019 08:11 UTC
  • Zarif Ya Gana Da Sayyid Hassan Nasrullah

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah a birnin Beirut.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a yayin ganawar, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana farin cikinsa dangane da kafa gwamnati a kasar Lebanon, tare da yin fatar samun nasarar gudanar da ayyukanta.

Haka nan kuma ya bayyanacewa, kasarsa a shirye take ta ci gaba da taimaka ma kasar Lebanon a dukkanin bangarorin da take bukatar taimako.

Haka nan kuma Zarif ya jaddada cewa siyasar kasarsa ita ce hankoron ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a cikin dukkanin kasashen yanin gabas ta tsakiya, da kuma ganin an samu fahimtar juna tsakanin gwamnatoci, gami da sauran bangarori na siyasa a cikin cikin dukkanin kasahen yanin, wanda a cewarsa hakan shi ne babban gishikin samun zaman lafiya a kasashen yankin baki daya.

Dangane da batun Palastine kuwa, Zarif ya bayyana cewa matsayar Iran kan hakan a fili take ga kowa a duniya, domin kuwa Iran ta yi imanin cewa Isra'ila ba halastacciyar kasa ce ba, kuma tana kira har kullum da a kafa kasar Palastine mai cin gishin kanta, wadda za ta kunshi dukkanin al'ummomi na asali da suke a yankin, da suka hada da larabawa musulmi da kirista, da kuma yahudawa 'yan asalin yankin.

Shi ma a nasa bangaren Syyid Hassan nNsrullah ya yaba da ziyarar ta Zarif, tare da bayyana goyon baya da kuma taimakon da Iran take baiwa kasar Lebanon da cewa, shi ne baban sirrin samun dukkanin nasarori a kan makiyan kasar musamman yahudawan sahyuniya.

Daga karshe Sayyid Nasrullah ya yi fatan samun nasara a cikin dukkanin lamurra da Iran ta sanya  agaba, da kuma taya dukkanin al’ummar kasar murnar zagayowar lokacin bukukuwan cikar shekaru arba’in na samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

Kafin ganawa da Sayyid Nasrullah, Zarif ya gana takwaransa na Lebanon Jubran Basil, kamar yadda kuma ya gana da shugaban kasar Michel Aun, gami da Firayi minister Sa'ad Hariri, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon Nabih Birri.

Daga bisani kuma Zarif ya gana da bangarori daban-daban na siyasa a kasar ta Lebanon, kamar yadda ya gana da wakilan kungiyoyin Falastinawa  a kasar, inda ya jaddada mahangar Iran kan cewa, dole ne al'ummar Palastine su kara hada kansu domin fuskantar kalu balen da ke gabansu, musamman kasancewar batunsu batu ne na musulmi da a dukkanin masu 'yanci na duniya baki daya.