Sojojin India, Pakistan Da Kuma Omman Suna Kabar Horo A Iran
Shugaban Makarantar Koyon aikin soje na kasar Iran DAFUS ya bayyana cewa dalibai masu koyon ayyukan soje daga kasashen waje da dama suna daukan horo a makarantun horar da sojoji a kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Brigadier Husain Zamani shugaban makarantar horar da sojoji wacce ake kira DAFUS yana fadar haka a safiyar yau Laraba.
Zamani ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran tana musayar sojoji da kasashen duniya da dama, sannan a nan Iran daliban kasashen waje suna koyin sabbin dubarun yaki, musamman wadanda a ke kira "yakin wakilci". Da kuma koyon irin korewar da sojojin Iran suke da shi a yake-yaken zamani, a rubuce a cikin aji, da kuma horaswa a aikace.
Kafin haka dai babban komandan sojojin kasar Iran Janar Sayyid Abdurrahim Musawi ya bayyana cewa sojojin kasashen waje da dama suna zuwa kasar Iran don samun horon ayyukan soje.
Janar Musawi ya kara da cewa kasar Iran tana da kayakin ayyukan horaswa da kuma malamai korarru wadanda suke da korewa a ayyukan yaki a jami'o'in horar da sojoji na kasar.