Iran: Jagoran Juyin Juya Hali Ya Jagoranci Dashen Itatuwa
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran yajagoranci dasa itatuwa a ranar dashen itatuwa ta kasa.
A jiya ne jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid ali Khamenei ya jagoranci dasa itatuwa a ranar dashen itatuwa ta kasa, tare da bayyana muhimamncin dashen itatuwa.
Ya ce ko shakku babu dashen itatuwa lamari ne mai matukar muhimmanci a cikin rayuwar dan adam, kamar yadda addini ma ya bayar da muhimmanci gad ashen itatuwa da kuma kula da su.
A lokacin da yake yin kira ga jami’an gwamnati a bangaren harkokin gandun daji, ya jadda kirasa garesu cewasu sani cewa aikinsu yana da babban muhimmanci a cikin al’umma, raya itatuwa bangare ne na raya al’umma.
Haka nan kuma ya ce sau da yawa akan shuka itaciya wadda baya ga inuwa da iskan da ta take samarwa mai tsafka da lafiya gad an adam, har ma wasu itatuwa suna bayar da ‘ya’yan marmari da dan adam ke bukata, kamar yadda kuma wasu suna samar da inuwa ne da iska da kuma kare Hamada.