Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Kasar Azarbaijan A Yau
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i3553-ministan_harkokin_wajen_iran_ya_gana_da_shugaban_kasar_azarbaijan_a_yau
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Azarbaijan a yau a birnin Baku fadar mulkin kasar ta Azarbaijna, kamar yadda ya gana da takwarorinsa na kasar ta Azarbaijan da kuma Rasha.
(last modified 2018-08-22T06:58:06+00:00 )
Apr 07, 2016 11:58 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Kasar Azarbaijan A Yau

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Azarbaijan a yau a birnin Baku fadar mulkin kasar ta Azarbaijna, kamar yadda ya gana da takwarorinsa na kasar ta Azarbaijan da kuma Rasha.

Kamfanin dillancin labaran Isna ya bayar da rahoton cewa, bangarorin uku na Iran, Rasha da kuma Azarbaijan, a yau sun tattauna muhimman lamurra da suka shafi kasashen uku da suke makwabtaka da tekun Caspian, musamman batun hanyoyin samar da zaman lafiya a yankin.

Kafin wannan ganawar dai minitocin harkokin wajen kasashen Rasha da Iran sun kirayi bangarorin Azarbaijan da Armenia da su kawo karshen yakin da suke yi, wanda kuam ake sa ran babbar manufar ziyarar ministocin harkokin wajen na Rasha da Iran zuwa Azarbaijan, ita ce sasanta kasashen biyu na Azarbaijan da Armenia.