Iran Ta Zargi Kasashen Yammaci Da Yada Kiyayya A Kan Musulunci
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya zargi kasashen yammacin turai da yada kiyayya ga musulmi ta hanyar siyasarsu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa dangane da harin ta'addancin da aka kai kan musulmi a kasar New Zealand, shugaba Rauhani ya bayyana lamarin da cewa abin bakin ciki ne da takaici.
Ya ce sau da yawa gwamnatocin kasashen yammacin turai suna bin wani salon siyasa wanda yake kunshe da nuna kyama ko wariya ga musulmi, wanda kuma irin wadannan hare-hare da ake kaiwa muuslmi sakamak ne na irin wannan siyasa.
Ya ce wajibi ne a kiyaye hakkokin musulmi a duk inda yake, kuma kasashen yammacin turai da suke raya kare hakkokin dan adam, abin takaici a cikin kasashensu en musulmi suka fi fuskantar irin wadannan ayyuka na nuna kyama da kiyayya a gare su.
Rauhani ya kara da cewa kisan musulmi New Zealand aiki ne na ta'addanci da dabbanci, wanda ya zama wajibi duniya ta yi Allawadai da shi, kuma a dauki matakan rayukan musulmi da dukiyoyinsu a duk inda suke a duniya.