Iran : Amurka Ba Za Ta Cimma Manufarta Ba Akan Iran_Ruhani
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i35613-iran_amurka_ba_za_ta_cimma_manufarta_ba_akan_iran_ruhani
Shugaban na kasar Iran ya kara da cewa; Al’ummar Iran mai dadadden tarihi ta jajurce da yin tsayin daka wajen kalubalantar Amurka, don haka Amurka ba za ta cimma manufarta ba.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 18, 2019 08:40 UTC
  • Iran : Amurka Ba Za Ta Cimma Manufarta Ba Akan Iran_Ruhani

Shugaban na kasar Iran ya kara da cewa; Al’ummar Iran mai dadadden tarihi ta jajurce da yin tsayin daka wajen kalubalantar Amurka, don haka Amurka ba za ta cimma manufarta ba.

Shugaban na kasar Iran ya bayyana haka ne a jiya Lahadi da yake bude sabbin wuraren hakar iskar Gas, dake kudancin kasar sannan kuma ya ce; Wannan rana ce ta farin ciki domin kuwa tana a matsyin nasara akan abokan gaba da basu son ci gaban Iran.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma bayyana cewa; Makiya sun tsammaci Iran za ta mika wuya saboda matsin lambar da masu girman kai na duniya suke yi mata, amma al’ummarmu wacce a tsawon tarihi ta yi tsayin daka, tana ci gaba da samun nasarori.