Zama Kan Harkokin Kasuwanci Da Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Sweden
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i6079-zama_kan_harkokin_kasuwanci_da_tattalin_arziki_tsakanin_iran_da_sweden
Manyan jami'an gwamnatocin kasashen Iran da Sweden suna gudanar da zaman tattaunawa a birnin Stockholm na kasar Sweden kan harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
Jun 01, 2016 05:27 UTC
  • Zama Kan Harkokin Kasuwanci Da Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Sweden

Manyan jami'an gwamnatocin kasashen Iran da Sweden suna gudanar da zaman tattaunawa a birnin Stockholm na kasar Sweden kan harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhamamd Jawad Zarif ne yake jagorantar tawagar kasar Iran, yayin da ministar harkokin wajen Sweden Ann Linde take jagorantar tawagar kasarta, jami'an gwanatocin Iran da Sweden 230 ne suke halartar zaman.

Tawagar Iran za ta halarci irin wannan zama a kasashen Holland, Filland, da kuma Lithuania, inda za a tatatuna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin na kasuwanci da tattalin arziki a tsakanin wadannan kasashe da kuma kasar ta Iran.