Sallar Juma'a A Tehran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i7498-sallar_juma'a_a_tehran
Hudubar Sallar Juma'a A Tehran
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jul 01, 2016 08:14 UTC
  • Sallar Juma'a A Tehran

Hudubar Sallar Juma'a A Tehran

Wanda ya jagoranci Sallar jumaa a yau ya bayyana cewa; Fadakar da musulmi su ke da ita ce ta hana, a maida batun palasdinu zama saniyar ware a duniya.

Ayatullah Ahmad Khatami wanda ya ke gabatar da huduba a yau juma'ar karshe ta watan Ramadhan wacce ita ce ranar qudus ta duniya, ya kara da cewa; Musulmi al'umma guda daya ce wacce ta ke karkashin inuwa guda, saboda haka ba za su taba samun nutsuwa ba matukar ba a 'yanto da palasdinu ba daga mamayar 'yan sahayoniya ba.

Gabanin Sallar juma'a a Tehran din miliyoyin al'ummar Iran sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin raya ranar qudus.

A cikin kasashe da dama na duniya an yi irin wannan zanga-zangar da su ka hada da Lebanon da kuma Yamen.