Zarif: Harin Bangaladesh Ya Kara Tabbatar Wajabcin Yaki Da Akidar Ta'adanci
(last modified Sun, 03 Jul 2016 17:48:38 GMT )
Jul 03, 2016 17:48 UTC
  • Zarif: Harin Bangaladesh Ya Kara Tabbatar Wajabcin Yaki Da Akidar Ta'adanci

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad Zarif ya kirayi al'ummomin duniya da su kara hada karfi da karfe, domin yaki da akidar ta'adanci a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Jawad Zarin ya yi wannan kira ne biyo bayan harin da aka kaddamar a birnin Daka na kasar Bangaladesh, inda ya ce wannan harin ya kara tabbatar wa duniya da cewa akidar ta'addanci ba ta da wata iyaka a kasashen duniya, har da ma wadanda suke da alaka da 'yan ta'adda lokaci na zuwa wanda su aknsu ba za su tsira daga sharrinsu ba.

 

Harin birnin Dakar na kasar Bangaladesh dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da ashirin, da suka hada da fararen hula da kuma jami'an tsaro, gami da 'yan ta'addan.

 

A akon da ya gabata ma an kai wani harin makamancin wannan a babban filin jiragen sama an Ataturk na birnin Istanbul na kasar Turkiya, inda mutane 44 suka rasa rayukansu.