-
Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Duk Wanda Ya Shiga Kasuwanci Da Iran Ba Zai Yi Da Amurka Ba
Aug 07, 2018 19:03Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa duk wata kasa da ta shiga harkar kasuwanci da kasar Iran gwamnatin Amurka zata daina kasuwanci da ita.
-
Shugaba Rauhani: Takunkumin Amurka Ba Zai Iya Karya Lagon Iran Ba
Aug 07, 2018 07:25A wata zantawa da da ya yi a daren jiya da tashar talabijin ta daya ta kasar Iran, shugaban kasar ta Iran Hassan Rauhani ya bayyana takunkumin da Trump ya kakaba wa kasar da cewa, ba zai iya karya lagon Iran ko durkusar da tattalin arzikinta ba.
-
Wani Tsohon Jami'in Amurka Ya Ce: Rashin Amincin Al'ummar Iran Kan Amurka Yana Da Tsohon Tarihi
Aug 06, 2018 12:03Wani tsohon jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya ce: Adawar al'ummar Iran kan kasar Amurka tana da tushe a tsawon tarihi musamman hannun da Amurkawa suke da shi wajen goyon bayan mulkin kama karya a kasarsu.
-
Iran : An Bude Taron Kasa Da Kasa kan Hakkin Bil'adama A Musulunci
Aug 04, 2018 11:48A safiyar yau Asabar ne aka bude taron kasa da kasa kan hakkin bil'adama a musulunci karo na ukku a nan Tehran.
-
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kan Masallacin Juma'a A Kasar Afganistan
Aug 04, 2018 07:01Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai wani Masallacin Juma'a a lardin Paktia na kasar Afganistan.
-
Jaridar The Wall Street Journal Ta Fallasa Makircin Amurka Da H.K.Isra'ila Kan Kasar Iran
Aug 04, 2018 06:57Jaridar The Wall Street Journal ta kasar Amurka ta fallasa makircin gwamnatin Amurka da na Haramtaciyar kasar Isra'ila kan zargin da suka yi cewa: Kasar Iran tana shirya kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasashen Turai.
-
Khudubar Jumma'a: Gwamnatin Iran Ba Za Ta Tattauna Da Amurka Ba
Aug 03, 2018 19:02Na'ibin limamin masallacin jumma'a a nan Tehran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran da shugaban kasar ba zasu sake shiga tattaunawa da gwamnatin Amurka ta yanzu ba.
-
Kasar China Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Na Dakatar Da Sayan Danyen Man Fetur Daga Kasar Iran
Aug 03, 2018 19:01Gwamnatin kasar China ta yi watsi da bukatar gwamnatin Amurka na ta dakatar da sayan danyen man fetur na kasar Iran, a kokarin da shugaban kasar ta Amurka Donal Trump yake yi na hana kasar Iran sayar da danyen man fetur kwata kwata nan da watan nuwamba mai zuwa a kasuwannin duniya.
-
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tir Da Takunkumin Amurka Akan Turkiya
Aug 02, 2018 18:49A yau alhami ne ministan harkokin wajen na IRan Muhammad Jawad Zarif ya rubuta yin Allah wadai da takunkumin a shafinsa na Twitter
-
Kioumars Heidari: Iran Tana Cikin Shirin Kare Kanta Daga Harin Wuce Gona Da Iri
Aug 02, 2018 07:43Kwamandan rundunar sojin kasa ta kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin shirin ko-ta kwana domin maida martani kan duk wani harin wuce gona da iri da zata iya fuskanta daga makiya.