Gyara Akan Furucin Ministan Harkokin Wajen Kasar Masar Akan Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10045-gyara_akan_furucin_ministan_harkokin_wajen_kasar_masar_akan_palasdinawa
Gyara Maganar Ministan Harkokin Wajen Masar
(last modified 2018-08-22T06:58:48+00:00 )
Aug 23, 2016 07:40 UTC
  • Gyara Akan Furucin Ministan Harkokin Wajen Kasar Masar Akan Palasdinawa

Gyara Maganar Ministan Harkokin Wajen Masar

Ma'aikatar harkokin Wajen kasar Masar ta ce; an sauya abinda ministan harkokin wajen kasar ya fada dangane da haramtacciyar Kasar Isra'ila.

Kamfanin Dillancin  Labarun Kasar Jamus, ya nakalto ministan harkokin wajen Masar Samih Shukry yana cewa; Hare-haren da 'yan sahayoniya su ka kai a bayan nan akan Palasdinawa, ba ta'addanci ba ne.

Su ma kafafen watsa labarun kasar Masar sun ambato Ministan harkokin wajen kasar tasu yana cewa; Matukar duniya ba ta bayyana ma'anar ta'addanci ba, to babu yadda za a bayyana kisan da 'yan sahayoniya su ke yi wa kananan yaran Palasdinawa, a matsayin ta'addanci.

A Palasdinu kungiyar gwagwarmayar palasdinawa ta Hamas ta maida martani akan furucin na Samih Shukry, inda kakainta Husam Badran ya ce: Mutumin da ba ya iya ganin laifukan 'yan sahayoniya to makaho ne.