Fashewar Bom A Kasar Lebanon
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10414-fashewar_bom_a_kasar_lebanon
A kalla mutum guda ne ya rasu a sanadiyyar tashin bom a Lebanon
(last modified 2018-08-22T11:28:51+00:00 )
Aug 31, 2016 19:04 UTC
  • Fashewar Bom A Kasar Lebanon

A kalla mutum guda ne ya rasu a sanadiyyar tashin bom a Lebanon

A kalla mutum guda ne ya rasu a sanadiyyar tashin bom a Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labarun Pars ya nakalto cewa; A yau laraba ne bom din y atashi a kauyen Zahlah da ke yankin Biqah a Lebanon wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu mutanen 4.

Bom din ya tashi ne akan hanyar da masu bikin zagayowar batan Imam Musa Sadr su ke bi a kudancin Lebanon.

Imam Musa Sadar wanda ya kafa majalisar koli na shi'a a Lebanon, tare da wasu mutane 2 a shekarar 1978 a kasar  Libya.

Har yanzu kungiyar Amal da gwamnati da al'ummar Lebanon suna kokarin sanin makomar shehun malamin daga gwamnatin Libya da aka kafa bayan kifar da Mu'ammar Kaddafi.