Hudubar Sallar Juma'a A Birnin Tehran Fadar Mulkin Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10498-hudubar_sallar_juma'a_a_birnin_tehran_fadar_mulkin_kasar_iran
Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewa: Al'ummar Iran ba zasu taba mancewa da kisan kiyashin da aka yi wa mahajjata a filin Mina a lokacin aikin hajjin shekarar da ta gabata ba.
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 02, 2016 13:03 UTC
  • Hudubar Sallar Juma'a A Birnin Tehran Fadar Mulkin Kasar Iran

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewa: Al'ummar Iran ba zasu taba mancewa da kisan kiyashin da aka yi wa mahajjata a filin Mina a lokacin aikin hajjin shekarar da ta gabata ba.

A hudubar sallarsa ta yau a babban Masallacin Juma'ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Ayatullahi Muhammad Ali Muwahhidi Kermoni ya tabo falalar watan Zul-Hijjah tare da muhimmancin aikin hajji a watan yana mai fayyace cewa: Kwararru kan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa; Da mahukuntan Saudiyya sun yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu a lokacin aikin hajjin shekarar da ta gabata, da ba za a kai ga samun turmutsutsin garin Minah da ya kai ga hasarar rayukan mahajjata da suka fito daga sassa daban daban na duniya ba.

Ayatullahi Muwahhidi ya kara da cewa: Aikin hajji rukuni ne na addinin Musulunci, don haka hakki ne da ke kan al'ummar musulmin a lokacin gamuwarsu a aikin hajji su dauki matakin tattauna irin matsaloli da barazanar da suke fuskanta daga makiya Musulunci tare da neman hanyar dinke baraka da rarrabuwar kai da ke tsakaninsu amma mahukuntan gidan sarautar Saudiyya sun katange al'ummar musulmi daga sauke wajibin da ya hau kansu.