Sojojin Siriya Sun Harbo Wani Jirgin Wani Jirgin Yakin Isra'ila
Sojojin kasar Siriya sun harbo wani jirgin yaki da kuma wani jirgin mara matuki na haramtacciyar kasar Isra'ila bayan wani hari da sojojin haramtacciyar kasar suka kai wa wani sansani na sojin Siriyan da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Siriyan SANA ya jiyo sojojin kasar suna fadin cewa sojojin sun harbo wadannan jiragen yakin ne bayan da suka shigo cikin kasar da kuma ci gaba da kai hare-hare kan wajajen da sojojin Siriyan suke. Majiyar ta kara da cewa an harbo jirgin saman yakin ne a yammacin yankin Quneitra da ke wajen birnin Damaskus.
Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra'ilan dai ta musanta wannan rahoton tana mai cewa sojojin Siriyan sun harba makamai masu linzami a kan jiragen na su amma dai ba su same su ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke musanta irin wadannan labaran ba, amma daga baya ta tabbata gaskiya ne.
A safiyar yau dai wasu jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ilan sun kai wasu hare-hare kan wajajen sojojin Siriyan a Tuddan Golan inda yankin na Qunetra yake.