Sake Bankado Boyayyiyar Alakar Dake Tsakanin 'Isra'ila' Da Mahukuntan Saudiyya
Cikin 'yan kwanakin nan dai bayanai sai dada fitowa suke yi dangane da boyayyiyar alakar da ke tsakanin haramtacciyar kasar Isra'ila da mahukuntan Al-Sa'ud na kasar Saudiyya; bayani na baya-bayan nan shi ne wanda jaridar Jerusalem Post ta Sahyoniyawan ta buga dangane da wata wasika da tsohon firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Ariel Sharon ya aika wa tsohon sarkin Saudiyyan Abdullah bn Abdul'aziz a watan Nuwambar 2005.
Jaridar ta taso da maganar wasikar ce bayan sukar 'Isra'ilan da yarima mai jiran gado na Saudiyyan Yarima Mohammed bin Nayef yayi a jawabin da yayi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniyan, don nuna tsohuwar alakar da ke tsakanin Saudiyyan da haramtacciyar kasar Isra'ilan. A cikin wasikar Ariel Sharon ya bayyana cewar: "Bisa la'akari da matsayin Saudiyya a yankin nan (Gabas ta tsakiya) da kuma irin hikima da hangen nesarka (sarki Abdullahin) a fagen siyasa, don haka mun yi amanna da cewa kasarka za ta iya taka gagarumar rawa wajen tabbatar da nasarar wannan shiri na sulhu (tsakanin Isra'ila da Palastinawa)".
Ariel Sharon ya rubuta wannan wasikar ce kimanin shekaru uku bayan da sarki Abdullahin ya gabatar da shirin sulhun larabawa da "Isra'ila" a shekara ta 2002 a taron shugabannin kungiyar kasashen larabawa da aka gudanar a birnin Beirut na kasar Labanon shirin da a zahiri Sharon din yayi watsi da shi, to sai dai wannan wasikar inji jaridar tana nuni da rashin ingancin batun da ake ta yayatawa na cewa haramtacciyar kasar Isra'ilan ba ta nuna wata alamar amincewa da shirin sulhun da Saudiyya din ta gabatar ba.
Wannan sabon fasa kwai dangane da irin boyayyiyar alakar da ke tsakanin 'Isra'ila' da Saudiyyan yana zuwa ne a daidai lokacin da a halin yanzu abin boyen ya fara fitowa fili tun bayan ziyarorin da Anwar ٍEshqi, tsohon janar din sojin Saudiyyan kuma tsohon mai ba wa Bandar bn Sultan, tsohon shugaban hukumar leken asirin Saudiyyan shawara, ya kai haramtacciyar kasar Isra'ilan, duk dai a kokarin da Saudiyyan take yi na kara samun kusaci da haramtacciyar kasar Isra'ilan.
Da dama dai suna ganin irin wadannan ganawa da take gudana tsakanin jami'an Saudiyya da na haramtacciyar kasar Isra'ila wanda tun da jimawa ake yin su a boye wani kokari ne da mahukuntan Saudiyyan suke yi a kokarinsu na yin sulhu da kuma dawo da alaka da gwamnatin Sahyoniyawan don cimma bukatun kasashen yammaci a yankin Gabas ta tsakiya da sauran kasashen musulmi. Don haka ne ma da dama suke ganin shirin sulhun da Saudiyyan ta gabatar a shekara ta 2002 din wani kokari ne na tilastawa kasashen larabawa su amince da halalcin haramtacciyar kasar Isra'ilan a hukumance da kuma dawo da alaka da ita; a bangare guda kuma da kawo karshen gwamnatoci da kungiyoyi masu gwagwarmaya da kuma adawa da bakar siyasar mamaya ta sahyoniyawan.
Wani lamari mai muhimmancin gaske kuma abin a yi dubi cikinsa cikin irin wannan lamarin shi ne irin ci gaba da mika kai da kasashen larabawa suke yi wa haramtacciyar kasar Isra'ilan da kuma irin boyayyiya da kuma bayyananniyar alakar da ke tsakaninsu da ita ta yadda a halin yanzu jami'an haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta maganar cewa nan gaba kadan da dama daga cikin kasashen larabawa za su dawo da alakarsu da ita. Irin wannan magana ta baya-bayan nan ita ce wadda ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ilan, Avigdor Lieberman, yayi na cewa cikin shekaru kadan za a yi sulhu tsakanin 'Isra'ila' da mafi yawa daga cikin kasashen larabawa.
Ko shakka babu ci gaba da irin wannan siyasa ta mika kai da neman sulhu da haramtacciyar kasar Isra'ila da wasu kasashen larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suke yi lamari ne mai hatsarin gaske ga lamarin Palastinawa da tabbatar musu da hakkokinsu da sahyoniyawa suka kwace, kamar yadda kuma lamari ne da zai kara sanya kasashen larabawan mika kai ga bakar aniyar sahyoniyawan da kuma tilasta musu gudanar da siyasar da ko shakka babu za ta zamanto mai cutarwa ga al'ummomin kasashensu da ma na sauran kasashen musulmi.
 
							 
						 
						