Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada A Gabar Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11800-wani_bapalasdine_ya_yi_shahada_a_gabar_yammacin_kogin_jordan
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan wani bapalasdine a gabar yammacin Kogin Jordan lamarin da ya janyo shahadarsa a jiya Juma'a.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Oct 01, 2016 02:05 UTC
  • Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada A Gabar Yammacin Kogin Jordan

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan wani bapalasdine a gabar yammacin Kogin Jordan lamarin da ya janyo shahadarsa a jiya Juma'a.

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan wani bapalasdine a gabar yammacin kogin Jordan a jiya Juma'a lamarin da ya yi sanadiyyar shahadarsa. Sojojin sun tsaurara matakan tsaro ne a dukkanin yankunan Palasdinawa da suka mamaye sakamakon jana'izar tsohon shugaban haramtacciyar kasar ta Isra'ila Shimon Peres da aka gudanar a jiya Juma'a.

Majiyar tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi da'awar cewa: Bapalasdinen yana kokarin kai hari ne kan tawagar sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila da suke sintiri a yankin garin Qalandiya da ke gabar yammacin kogin Jordan.

A jiya Juma'a ce aka gudanar da jana'izar tsohon shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila Shimon Peres da ya mutu a ranar Larabar da ta gabata yana da shekaru 93 a duniya. Peres ya taka gagarumar rawa a fagen aiwatar da bakar siyasar zalunci da kisan gilla kan al'ummar Palasdinu, kuma daga cikin mahalatta jana'izarsa a jiya har da shugaban kasar Amurka Barak Obama da na Faransa Francois Hollande gami da na Jamus Joachim Gauck, haka nan shugaban hukumar Palasdinawa Mahmud Abbas da tawagarsa.