Matsayar Shugabanni da Al'ummar Larabawa Kan Mutuwar Shimon Peres.
A daidai lokacin da al'ummar Palastinu da kungiyoyin gwagwarmayar Palasatinawa suke ci gaba da nuna farin cikinsu dangane da mutuwar tsohon firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Shimon Peres, a bangare guda kuma wasu daga cikin shugabannin larabawan kuwa sai nuna aihininsu suke yi dangane da wannan mutuwar, lamarin da ke sake tabbatar da irin tazarar da ke tsakanin shugabannin larabawan da al'ummomin da suke ikirarin suna jagoranta.
A ranar 28 ga watan Satumban nan ne dai aka sanar da mutuwar Peres bayan makonni biyu na tsananin rashin lafiya sakamakon mummunan bugun zuciyar da yayi fama da shi da yayi sanadiyyar shanyewar jikinsa. Duk da cewa mutuwar Peres ta kasance abin faranta rai ga da dama daga cikin al'ummar larabawa, to sai dai wannan farin ciki ya kasance tare da wani abin mai sosa rai, wanda hakan kuwa shi ne irin sakon ta'aziyya da nuna alhinin da wasu shugabanni da jami'an larabawa suka yi dangane da mutuwar mutumin da rayuwarsa cike take da ayyukan ta'addanci da zubar da jinin dubun dubatan al'ummar larabawan musamman Palastinawan cikinsu.
A yayin da yake aikewa da sakon ta'aziyyarsa dangane da mutuwar Peres din, ministan harkokin wajen kasar Bahrain Khalid bn Ahmad Al Khalifa ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Allah Ya jikan shugaba Shimon Peres, mutum ma'abocin yaki kana kuma ma'abocin zaman lafiyan da har ya zuwa yanzu samunsa ke da wahala a Gabas ta tsakiya".
Shi ma a nasa bangaren, shugaban hukumar cin gashin kan Palastinawa Mahmood Abbas, wanda har halartar jana'izar Peres din ma yayi ya bayyana, cikin wani sako na ta'aziyya da ya fitar ya bayyana bakin cikinsa dangane da mutuwar Peres din wanda ya bayyana shi a matsayin "abokin tafiya wajen tabbatar da zaman lafiya tare da tsohon shugaban Palastinawa Yasser Arafat da firayi ministan "Isra'ila" Yitzhak Rabin".
Sanannen dan majalisar haramtacciyar kasar Isra'ila (Knesset) daga jam'iyyar Likud, Ayoob Kara ya bayyana cewar shugabannin daya daga cikin kasashen larabawan Tekun Fasha a lokacin da ya ji labarin mutuwar Peres sai da yayi kuka.
Har ya zuwa yanzu dai al'ummar larabawa musamman Palastinawa suna ci gaba da Allah wadai da wannan matsaya da mahanga ta shugabannin larabawan musamman na Mahmood Abbas saboda irin ganin da suke yi wa Shimon Peres din a matsayin babban mai laifi wanda yayi sanadiyyar zubar jinin dubun dubatan Palastinawa kamar yadda kungiyar Hamas ta bayyana.
A daidai lokacin da wasu daga cikin shugabannin larabawan suke bayyana aihini da damuwarsu dangane da mutuwar Shimon Peres da bayyana shi a matsayin ma'abocin zaman lafiya, shi kuwa sanannen marubuci da sharhi kan yankin Gabas ta tsakiya Robert Fisk, cikin wata makala da ya rubuta a jaridar Independent, cewa yayi sabanin abin da shugabannin larabawa suke kokarin nunawa, lalle Shimon Peres bai kasance ma'abocin sulhu da zaman lafiya ba. Mr. Fisk ya ci gaba da cewa: To amma ni a lokacin da na sami labarin cewa Peres ya mutu, abin da ya fara zuwa min shi ne tunanin jini, wuta da kuma kisan gilla. Don kuwa na ga ayyukansa. Na ga karamin yaron da aka yi kaca-kaca da namansa".
To abin tambayar dai a nan shi ne mene ne dalilin irin wannan bambancin mahanga da aka samu tsakanin shugabannin larabawa da al'ummominsu da kuma masana da marubutan larabawan har ma da na kasashen yammaci? Sannan kuma shin shugabannin larabawan ne suka sauya ko kuma dai "Isra'ila" din ce ta sauya da har ta fara samun yabo daga wajensu?
Dubi cikin shekarun 1950, 1960 har zuwa karshe-karshen 1970 za mu ga cewa nuna rashin amincewa da samuwar "Isra'ila" da kuma yin Allah wadai da danyen aikin da take yi bugu da kari kan goyon bayan al'ummar Palastinu su ne manyan abubuwan da suke kawo musu halalci da matsayin a zukatan al'ummominsu, hakan ne ma ya sanya su yaki da haramtacciyar kasar Isra'ilan a shekarun 1967 da 1973.
To sai dai kuma irin wannan kishin ya fara ja da baya tun daga shekarun 1970 din lamarin da ya haifar da yarjejeniyar sulhu ta Camp David, da kuma na Madrid da Oslo a shekarun 1990, wanda da dama daga cikin Palastinawa da ma al'ummar larabawan suke ganinsu a matsayin cin amana kana kuma wani mataki na kusatar sahyoniyawa 'yan mamaya da kuma yin watsi da lamarin Palastinawan.
Hakan kuwa ta faru. Don kuwa tun ba a je ko ina ba kasashen Jordan da Qatar suka bude ofisoshin kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra'ilan a kasashensu, don share fagen kulla alaka ta diplomasiyya da ita. Wasu kasashen larabawan kuma a boye suka ci gaba da yin hakan.
Hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da haramtacciyar kasar Isra'ilan ba ta rage komai kashin irin danyen aikin da take aikatawa a kan al'ummar Palastinu kai har ma da na Labanon ba, face ma dai ta ci gaba da kara kaimi ne wajen aikata hakan da kuma ci gaba da gina matsugunan yahudawa da nufin ci gaba da korar Palastinawa daga kasarsu.
A saboda haka ko shakka babu, ba 'Isra'ila' da sahyoniyawa din ne suka sauya ko kuma suka rage irin danyen aikin da suke aikatawa ba, face dai shugabannin larabawan ne suka sauya ko kuma alal akalla suka fara bayyanar da hakikaninsu ga al'ummomin da suka jahilce su.
Da dama dai suna ganin babban dalilin irin wannan sauyi da shugabannin larabawan suka yi shi ne cewa suna ganin ci gaba da zamansu a kan kujerar mulkinsu ya damfaru ne da goyon bayan kasashen yammaci musamman Amurka. Don kuwa babban sharadin Amurka wajen goyon bayansu, shi ne zaman lafiya da haramtacciyar kasar Isra'ila.